Ronaldo zai yi wa Madrid wasa a ranar Laraba

Asalin hoton, Real Madrid
Real Madrid za ta fara wasan farko a cikin rukuni a gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana a ranar Laraba a kokarin kare kambunta.
Madrid wadda ke da kofin guda 12 a tarihi, za ta karbi bakuncin APOEL Nicosia a Santiago Bernabeu, kuma wata kila Cristiano Ronaldo ya buga karawar.
Ronaldo bai buga wa Madrid wasa hudu ba, sakamakon dakatar da shi da aka yi, bayan da ya ture alkalin wasa a karawa da Barcelona a gasar Spanish Super Cup.
Sai dai hukuncin hana shi buga wa Madrid wasa biyar bai shafi na gasar Zakarun Turai ba, kuma saura wasa daya ya kammala hukuncin da hukumar kwallon Spaniya ta yanke masa.
Madrid ta buga wasa 14 a jere a gida ba a doke ta ba a gasar ta Zakarun Turai, tun bayan rashin nasara da ta yi a hannun Schalke a 2015.
Ga jerin wasannin Madrid na cikin rukuni a gasar Zakarun Turai:
- Laraba 13 ga watan Satumba Real Madrid-APOEL
- Talata 26 ga watan Satumba Borussia Dortmund-Real Madrid
- Talata 17 ga watan Oktoba Real Madrid-Tottenham
- Laraba 1 ga watan Nuwamba Tottenham-Real Madrid
- Talata 21 ga watan Nuwamba APOEL-Real Madrid








