Barcelona za ta karbi bakuncin Juventus

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Mohammed Abdu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- An wallafa
Juventus za ta ziyarci Barcelona a ranar Talata a wasan rukuni na hudu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta 2017/18.
Kungiyoyin biyu sun kara a wasannin Zakarun Turai sau 11, inda Juventus ta ci karawa biyar, Barcelona ta ci wasa uku suka yi canjaras a fafatawa uku.
A gasar da aka kammala Juventus ta ci Barca 3-0 a Italiya, sannan suka tashi 0-0 a Spaniya, hakan ya sa Barcelona ta yi ban kwana da kofin da Real Madrid ta ci kuma na 12 jumulla.
A dai karawar ta rukuni na hudun, Olympiacos ta Girka za ta kece raini da Sporting ta Portugal.
Ga sauran wasannin da za a buga a ranar Talata:
- Chelsea FC Qarabag Agdam FK
- Manchester United FC Basel 1893
- AS Roma Atletico de Madrid
- Bayern Munich RSC Anderlecht
- Celtic Paris Saint-Germain
- Benfica CSKA Moscow








