Koci hudu aka kora a Premier shekarar nan

Premiere

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bayan da aka buga wasan mako na 11 a Premier an koci koci hudu
An wallafa

Bayan da aka kammala wasannin mako na 11 a karshen sati a gasar cin kofin Premier bana, an sallami koci hudu a kakar 2017/18.

Kocin Crystal Palace, Frank De Boer aka fara sallama a ranar 11 ga watan Satumba, bayan da ya yi kwana 77 a kan aikin

Craig Shakespeare shi ne na biyu da aka sallama a ranar Talata 17 ga watan Oktoba, bayan da ya yi kwana 236 yana jan ragamar Leicester City.

Koci na uku da aka sallama daga aikin horar da tamaula a Premier shi ne Ronald Koeman, wanda aka kora a ranar Litinin 23 ga watan Oktoba, bayan kwana 496 da ya yi a kan aikin.

Slaven Bilic shi ne na hudu da ya bar aiki a Premier a bana, bayan da West Ham ta sallame shi a ranar Litinin 6 ga watan Nuwamba, bayan kwana 881 yana gudanar da aikin.