Young ya tsawaita zamansa a United

Ashley Young

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United ta sanar cewar mai tsaron baya Ashley Young ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara daya, domin ci gaba da taka-leda a kungiyar.

Dan wasan mai saka riga mai lamba 18, zai ci gaba da zama a United har zuwa karshen kakar 2019/20.

Young ya ci kwallo 17 a wasa 227 da ya buga wa United tun komawarsa Old Trafford daga Aston Villa a 2011.

Dan wasan mai shekara 33, ya lashe Community Shield da Premier League da FA da League Cup da kuma UEFA Europa League.