Abin da ya sa maza da mata ba sa buga kwallo tare

Stephanie Labbe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yar wasa mai tsaron gida Stephanie Labbe an hana ta wasa tare da mazan kungiyar Amurka
    • Marubuci, Daga Fernando Duarte
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Stephanie Labbe fitacciyar 'yar kwallo ce, madallah da kwarewarta a matsayin mai tsaron raga.

Nasarar da Kanada ta samu a kan Kamaru da ci 1-0 a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2019 ranar Litinin ta sa ta samu nasarori 30 cikin wasanni 62 da ta yi wa Kanada - hakan na nufin ba ta bar kwallon ta shiga raga a kusan rabin wasanni da ta yi wa kasarta ba, kuma hakan bajinta ce ta girmamawa a gare ta.

Amma Labbe ta mamaye kanun labarai da dama, madallah da kokarin da ta yi na shiga tawagar maza ta Calgary Foothills, wata 'yar karamar kungiyar kwallo ta Kanada - da ke wasa a matakin Lig na biyu USL, na Amurka.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Mai tsaron ragar dai ta samu shiga tawagar har ma ta yi musu wani wasan sada zumunci, ta fara abin kirki, kafin daga bisani hukumomi su haramta mata ci gaba da wasa a tawagar mazan - inda suka ce gasar USL ta maza ce zalla.

Maribel Dominguez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fifa ta kare tsarinta na raba jinsi inda ta hana Maribelbuga wasa tare da mazan kungiyar kasar Mexico

A yanzu da take da shakera 32, Labbe ta zama ta baya-bayan nan da take kalubalantar nuna wariyar jinsi da ake yi a cikin mahukuntan wasan kwallo.

Duk da cewa hukumomin kwallo na kasashe da dama sun daga batun rage yawan shekaru a tawagar hadaka ta maza da mata a tawagogin matasa, har yanzu hakan haramtaccen abu ne a wasan kwallo.

Akidar nuna wariya

A shekarar 2004 hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta bayyana cewa "dole a ware tsakanin mata da maza a wasan kwallo."

Kalaman, martani ne da ke hade da hawa kujerar na ki da hukumar ta Fifa ta yi game da bai wa 'yar wasan Mexico Maribel Dominguez da kungiyar kwallon kafa ta maza Celaya ta yi.

Fifa ta yanke hukuncin inda ta gasgata Dominguez kamar yadda kungiyar kwallon kafa ta Mexico ta ce. Sannan ta jaddada cewa raba wasa tsakanin jinsi muhimmi ne a wasan kwallo.

Marta facing a male opponent

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marta ta buga wasan sada zuminci a 2014 tare da 'yan wasa kamar Zinedine Zidane da Ronaldo

"An sanya wannan a cikin tsarin gasanni da kuma wasannin kasa da kasa na ware jinsi, kuma babu wata dokar wasan ko ta FIFA da ta yi sassauci a kan hakan," a cewar hukumar wasan.

Wannan kuma shi ne ra'ayin jama'a kuma maganar ita ce kirar jikin maza da mata ta bambanta haka zalika ma kuzarinsu.

Sauyi a Olympic

A wasu wasannin akwai bambancin aiki a tsakani: a cewar wani bincike na mujallar magungunan kimiyyar wasanni, a wani gwajin da ta yi tsakanin maza da mata ta gano cewa maza na iya fin mata kuzarin wasa har zuwa kimanin kashi 40 fiye da na matan.

Kuma cakuduwa tsakaninsu ba ta haduwa a mafi yawancin manyan wasannin duniya.

Mixed doubles tennis match

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tennis na daya daga cikin wasannin da maza da mata ke bugawa a tare

A wasannin Summer Olympic, suna karawa amma ana hada su ne tare da namiji inda shi ma wani tare da mace, kamar a wasan Tennis da Badminton.

A 2017, kwamitin Olympic na kasa da kasa ya bayyana cewa a wasan Tokyo 2020 za a hada maza da mata a wasan gudu da wasan ninkaya a ruwa.

Wasan kwallo ba shi da bambanci a wajen kuzari a tsakanin jinsi a cewar kimiyya.

Paul Bradley, masanin wasanni a jami'ar John Moore da ke a Liverpool, ya yi bincike da yawa a kan wasan kwallon kafa na mata, wanda ya hada da wata makala ta 2013 wadda ta yi duba tsakanin gasar Uefa ta maza da ta mata.

Mixed training in France

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu kasashe na kara yawan shekarun da maza da mata za su iya buga wasa a tare

Bradley da mutanensu sun yi kokari sosai a yunkurinsu, a wajen gudu da tsalle-tsalle.

Amma binciken ya nuna cewa mata sun fi maza hazaka. Masu bincike na ganin cewa wasan mata na kusan kamo na maza.

"Ganin yadda kwarewar wasan mata ke sauyawa a shekarun nan, a 'yan shekaru masu zuwa muna tsammanin za a sauya alkaluman gwajin jiki," Bradley ya shaida wa BBC.

"Musamman idan aka ba su horo a kimiyyar wasanni da karfi da gina jiki da kuma horo na musamman."

Girl is chased by a boy on a football pitch

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan wasa marasa jiki da gudu sun ba da mamaki inda a tarihi suka samu nasarori sosai wanda hakan ke nuni cewa maza da mata za su iya buga kwallo a tare

Kwakwalwa ko karfi?

'Yan wasa marasa jiki da gudu sun ba da mamaki inda a tarihi suka samu nasarori sosai wanda hakan ke nuni cewa maza da mata za su iya buga kwallo a tare.

Misali na musamman shi ne 'yar wasan da ta ci kambun 'yar wasan duniya sau shida Marta.

'Yar wasan a watan Disamba ta bayyana cewa ba za ta ki tayin buga wasa tare da maza ba.

"Na buga wasa sau da dama tare da maza kuma wasu sun fi ni karfi da tsayi. Na san a filin wasa za su iya buge ni amma ina amfani ne da kwakwalwata.

Japanese player with an injury

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan wasa mata sun fi yiyuwar samun rauni idan ana wasa

Inda take magana a kan abin da ta fuskanta a watan da ya gabata a Calgary Foothills, Stephanie Labbe ta bayyana cewa ba za ta iya karawa da maza ba saboda kirar jikinsu.

"A matsayin mai tsaron gida, ina ganin yana da dama saboda kana fuskantar kwallo mai guda ne, mai karfi kuma, kuma wasan na da sauri sosai" take gaya wa kamfanin dillancin labaran Faransa.

Amma duk da haka, da ta ci gaba da wasan idan da hukumomin wasan ba su hana ta ba.

"Abin takaici ne a ce maka ba za ka iya buga wasan ba saboda wani abu da ba laifinka ba," a cewar Labbe.

Fifa headquarters in Zurich

Asalin hoton, Getty Images

"Wannan ba wani abu ba ne da zan iya zuwa gida in sauya. Jinsina jinsina ne."

Federicco Luzzi, masanin falsafa a Jami'ar Aberdeen da ke Scotland, ya kira raba tsakanin maza da mata da FIFA ke yi a matsayin "rashawar wasanni wadda ba a lura da ita ba."

"Ko da babu wata mace kwararra a wasan kwallon kafa kamar kwararren namiji, bai kamata hukumomin kwallo su hana sayen wani dan wasa saboda rashin hazakarsa ba, a cewarsa.

Masu goyon bayan rabawa tsakanin jinsi sun ce ya fi wa mata tsaro, inda suka bayyana cewa mata masu wasan kwallon kafa sun fi yiyuwar samun rauni fiye da maza, kamar a guiwa da kafafuwansu saboda bambancin kirar jikinsu.

Australian footballers in training

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasan kwallon kafa ba na jiki ba ne kawai

Game da gocewar kafa, wani bincike da FIFA ta kaddamar ya nuna cewa mata sun fi yiyuwar samun hakan sau biyu zuwa shida a kan maza.

"Ko da mata sun fi yiyuwar samun rauni, ba za a lamunta da matakin dakatar da mata ba. Idan aka yi haka, su ma maza masu yiyuwar samun rauni ya kamata a hana su," a cewar Luzzi.

Amma samun kasashe kamar su Ingila da Holand da Jamus sun kara da cewa lokacin kwallon kafa tsakanin maza da mata suna kanana zai haifar da al'ummar da za ta ki amincewa da raba su saboda jinsi, a cewar Jean William, wata farfesar wasanni a Jami'ar Wolverhampton.

Boys and girls playing football

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yara masu tasowa za su saba ganin wasa tsakanin maza da mata a hade

"Samun cakuduwa a wasan kwallon kafa zai daidaita tunanin wasa tsakanin maza da mata. Zai yi wahala ga 'yan baya su amince da raba su a nan gaba," a cewarta.

"Akwai bukatar mu ga mata da yawa suna kalubalantar raba wasan kwallon kafa. Akwai sauye-sauye da yawa da za su auku nan da shekara 10 masu zuwa."