Man United ta amince ta sayar da Young

Asalin hoton, AFP
ManchesterUnited ta amince ta sayar wa Inter Milan Ashley Young kan fam miliyan 1.28.
Tun a baya Young mai shekara 34, ya shaidawa United aniyarsa ta son zuwa Inter, hakan ne ya sa ba ta yi amfani da shi a wasa uku baya ba.
Dan wasan zai kawo karshen buga leda na tsawon shekara takwas da rabi da ya yi a Old Trafford.
Yarjejeniyar daukar dan wasan ta tattara ne da zarar Inter Milan ta auna koshin lafiyarsa ranar Litinin.
Young ya buga wa United wasa 261, kuma shi ne kyaftin a kakar bana, sai dai wasa 10 kacal aka fara da shi a kakar.
Wanda ya yi wa Ingila wasa 39 ya koma Old Trafford daga Aston Villa a 2011, ya kuma ci kofin Premier a 2012/13 da FA Cup a 2015/16 da League Cup da na Europa a 2016/17.
Inter wadda ta dauki Romelu Lukaku da kuma aron Alexis Sanchez tana ta biyu a teburin Serie A da tazarar maki biyu tsakaninta da Juventus ta daya.












