Pogba ba mallakin Solskjaer bane in ji Raiola

Asalin hoton, Getty Images
Mai kula da harkokin tamaular Paul Pogba ya ce dan wasan tawagar Faransa ba mallakin Ole Gunnar Solksjaer bane.
Pogba, mai shekara 26, na yin jinya, amma Mino Raiola ya ce watakila dan wasan ya sake komawa Juventus a karshen kakar bana.
Solskjaer ya mayar da martani cewar bai yi magana da Raiola ba, amma dai Paul dan wasanmu ne ba na Minos ba.
A wani sako da Raiola ya rubuta a kafar sada zumuntarsa ya ce yana fatan Solskjaer bai mayar da ''Paul fursunansa ba''.
Raiola ya mayar da cewar ''Paul ba na shi bane ya kuma tabbatar ba mallakin Solskjaer bane, amma Paul ai Pual Pogba ne.
Pogba ya buga wa United wasa takwas a kakar bana da kuma biyu tun watan Satumba.
Wasan karshe da ya yi wa Manchester United shi ne a karawar da United ta doke Newcastle da ci 4-1 ranar 1 ga Kirsimeti.








