French Open: Rafael Nadal ya doke Novak Djokovic inda ya lashe French Open karo na 13

Asalin hoton, EPA
An wallafa
Rafael Nadal ya lashe gasar kwallon tennis ta French Open ta bana, bayan da ya doke Novak Djokovic ya kuma yi kan-kan-kan da Roger Federe wajen lashe manyan gasar tennis 20 jumulla.
Dan kasar Sifaniya wanda yake na biyu a jerin wadanda ke kan gaba a wasan a duniya, ya doke na daya wato Djokovic da ci 6-0, 6-2, 7-5 kuma karo na 13 da yake zama zakara a gasar.
Wannan ne karon farko da Djokovic, mai shekara 33 ya yi rashin nasara a dukkan fafatawar a kakar 2020.
Tun farko, Djokovic wanda ya lashe manyan gasar tennis 17, ya yi kokarin neman na 18 a Paris, hakan bai yi wu ba, bayan da Nadal ya yi nasara ya kuma lashe babbar gasa ta 20 kenan.
Nadal ya yi nasara ne bayan awa biyu da minti 41.









