Mohamed Salah: An dakatar da wanda ya yi wa dan kwallon Liverpool kalamun nuna wariya

Mohamed Salah

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

An dakatar da wani mai goyon bayan West Ham United daga shiga sabgogin tamaula zuwa shekara uku, bayan da ya tabbatar ya yi wa Mohamed Salah kalaman nuna wariya da cin zarafi.

A watan Fabrairun 2019 a lokacin da Liverpool ta tashi 1-1 a gidan West Ham, an nadi faifan bidiyon Salah a wayar salula a lokacin da zai dauki kwana.

An kuma nadi murya ta cin zarafi da kalaman wariya a kan bidiyon da aka yi wa Salah da addininsa na musulunci.

A wata kotun majistire, Bradley Thumwood, mai shekara 48 ya amsa laifin yin kalaman wariya da cin zarafi.

An kuma ci tarar Thumwood fam 400 an kuma bukaci da ya biya Salah kudin kara da dawainiya da ya kai fam 125.