Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Messi da Van de Beek da Saul da Johnstone da Pogba, Ziyech da Coutinho

Messi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Paris St-Germain ta mika tayi ga ɗan wasan Argentina mai shekara 34, Lionel Messi, wanda ba shi da wata ƙungiya bayan kwantiraginsa na Barcelona ya kare. Ƙungiyar ta La Liga na da ƙarfin gwiwar za ta cimma nasarar dauke ɗan wasan da ya lashe kyautar Ballon d'Or sau shida. (AS - in Spanish)

A shirye Manchester United take ta bar Donny van de Beek ya bar kungiyar a wannan kakar, yayin da Real Madrid ta nuna sha'awarta kan ɗan wasan mai shekara 24. (Star)

Barin Van de Beek ƙungiyar, zai ba da damar dauko ɗan wasan Madrid Raphael Varane, mai shekara 28. (Sun)

Liverpool na farautar ɗan wasan Atletico Madrid mai buga tsakiya, Saul Niguez.(La Razon - in Spanish)

Arsenal a shirye take ta dauko mai tsaron ragar West Brom da Ingila Sam Johnstone, muddin aka daidaita da Sheffield United kan Aaron Ramsdale mai shekara 23. (Star)

Liverpool na son ɗauko ɗan wasan Lille asalin Portugal Renato Sanches, sai dai akwai yiwuwar ta fuskanci gasa daga Arsenal da Bayern Munich.(Onze Mondial - in French)

Kocin Juventus Massimiliano Allegri ya sanar da aniyarsa ta sake ɗauko ɗan wasan Manchester United, Paul Pogba. Ɗan wasan mai shekara 28 da yarjejeniyarsa da Old Trafford ke ƙarewa a 2022, sau biyu ya lashe kambun Serie A. (90 Min)

Hakim Ziyech ya ja hankalin AC Milan, wanda ke kallon ɗan wasan na Chelsea mai shekara 28 a matsayin wanda yafi dacewa ta sayo a kan ɗan wasan EvertonJames Rodriguez. (Corriere dello Sport via Sport Witness)

Ko da yake itama Milan ta ƙarbi tayi kan ɗan wasan Brazil Philippe Coutinho daga Barcelona.(Mundo Deportivo - in Spanish)

Ɗan wasan tsakiyar Norway Martin Odegaard, ya ba da tabbacin cewa ba zai koma Arsenal ba a kaka mai zuwa bayan ɗaukan tsawon lokaci na zaman aro a London daga Real Madrid. (Football London)

Kocin Burnley Sean Dyche na tuntuɓa kan sayen ɗan wasan nan mai shekara 31 Marc Albrighton daga Leicester.(Sun)

Ɗan wasanBayer Leverkusen asalin Jamhuriyar Czech, Patrik Schick, ya kasance wanda AC Milan ke hari a yanzu. (Tuttomercatoweb - in Italian)

Inter Milan ta shiga tattaunawa da wakilan Denzel Dumfries' inda take fatan daidaitawa da kungiyarsa PSV Eindhoven.(Calciomercato via Football Italia)

Tottenham na zawarcin ɗan wasan Fiorentina Dusan Vlahovic, sai dai hankalin ɗan wasan ya karkata kan sake sabunta kwantiraginsa da kungiyarsa ta Seria A. (Corriere dello Sport via Sport Witness)

Mai buga wa Arsenal tsakiya Matteo Guendouzi, na dab da koma wa Marseille yayin da ake saran kulob din ya kuma kammala yarjejeiyar dauko dan wasan Gunners din William Saliba, mai shekara 20. (Goal)