Junior Firpo: Mai tsaron bayan Barcelona ya koma Leeds United

Asalin hoton, Getty Images
Leeds United ta dauki mai tsaron baya Junior Firpo daga Barcelona kan fam miliyan 13 kan yarjejeniyar shekara hudu.
Mai shekara 24 ya koma Nou Camp da taka leda daga Real Betis a kakar 2019, wadda ya yi wa Barca wasa 41.
Tsohon matashin dan wasan tawagar Sifaniya ta matasa 'yan shekara 21 ya lashe Copa del Rey a Barcelona a kakar da aka kammala.
Firpo, wanda aka haifa a Jamhuriyar Dominican ya koma Sifaniya yana da shekara shida da haihuwa, yana kaunar salon kocin Leeds United, Marcelo Bielsa.
Shi dai Bielsa ya horar da tamaula a kungiyoyin Sifaniya da suka hada da Espanyol da kuma Athletic Bilbao.
Leeds United za ta fara jiyartar Manchester United ranar 14 ga watan Agustan, 2021 a karawar farko a gasar Premier ta 2021/22.








