Scolari ya karbi aikin horar da Gremio karo na hudu

Luiz Felipe Scolari

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Luiz Felipe Scolari ya karbi aikin kocin Gremio karo na hudu da zai ja ragamar kungiyar, kamar yadda ta sanar ranar Laraba.

Tsohon kocin Chelsea da tawagar kwallon kafa ta Portugal da ta Brazil ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen Disambar 2022.

Ya karbi aikin da sharadin zai hana kungiyar faduwa daga gasar kwallon kafar Brazil, inda Gremio ke mataki na karshe da maki biyu, bayan wasa takwas.

A karo uku da ya horar da kungiyar, Scolari ya lashe kofin gasar Brazil da kofin kalubale da kuma Copa Libertadores, wanda yake mataki kamar Champions League.

Mai shekara 72 ya fara horar da Gremio a 1987 ya kuma ce ita ce kungiyar da yake ji tamkar gida a wajensa.

Kungiyar karshe da ya horar ita ce Cruzeiro a farkon shekarar nan, ya kuma horar da Gremio kungiyar Brazil a 1993 da kuma a 2014.