Nacho zai ci gaba da taka leda a Real zuwa 2023

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron baya, Nacho Fernandez ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Real Madrid zuwa karshen kakar 2023.
Ya koma Real a shekarar 2001, yana da shekara 11, wanda ya fara daga makarantar kungiyar har zuwa Castilla daga nan ya fada babbar Real Madrid.
Nacho ya fara buga wa babbar kungiyar Real wasa cikin Afirilun 2011 a karawa da Valaencia a La Liga, wanda Madrid ta je ta yi nasara da ci 6-3.
Tun daga lokacin Nacho, wanda ya lashe kofi 17 ya ci gaba da taka rawar gani a kungiyar, cikin kofunan da ya lashe sun hada da Champions League hudu da Club World Cup da UEFA Super Cup uku.
Sauran sun hada da La Liga biyu da Copa del Rey da kuma Spanish Super Cup uku da ya lashe a Real Madrid.
Kawo yanzu Nacho shine wanda ya fi dadewa a Real Madrid, wanda ya buga mata karawa 233, ciki har da wasa 158 a La Liga da 41 a Champions League.
Mai tsaron bayan ya buga wa Real wasa 30 a Copa del Rey da uku a World Club Cup da karawa daya a Spanish Super Cup.
Nacho wanda yake kaka ta 20 a Real Madrid ya ci mata kwallo daya tal.












