Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Di Lorenzo, Haaland, Kane, Camavinga, Emerson, Zidane, Giroud, Benzema

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta kwaɗaitu da ɗan wasan Napoli da ake maganar cinikinsa kan £17m, Giovanni di Lorenzo bayan kammala wasan Championship na Ingila a wannan Lahadin. (Il Napolista, via Sun on Sunday)
Kocin Chelsea Thomas Tuchel na son a gaggauta mara masa baya wajen ɗauko ɗan wasan Norway Erling Braut Haaland da ke taka leda a Borussia Dortmund.(Bild - in German)
Manchester United ba ta wani taka rawar gani kan yarjejeniyar musayar ƴan wasanqw domin dawo da ɗan wasan Ingila Harry Kane zuwa Tottenham. (Sunday Express)
Chelsea ta tuntubi Rennes kan cinikin ɗan wasan nan da ke buga tsakiya Eduardo Camavinga, ɗan shekara 18. Burin ɗan wasan shi ne koma wa Manchester United, Arsenal ko Real Madrid ko da yake ya ce ya fi son zama a Faransa saboda Paris St-Germain. (Le Parisien - via Sun on Sunday)
Kocin Everton Rafael Benitez na son ɗauko ƴan wasan baya, kuma hankalinsa ya karkata kan ɗan wasan Norwich City Max Aarons da Dutchman Denzel Dumfries daga PSV Eindhoven. (90mins)
Napoli ta dage wajen ganin ta yi nasarar ɗauko ɗanwasan Chelsea Emerson Palmieri. (Corriere dello Sport - in Italian)
West Ham ita ma yanzu haka hankalinta ya koma kan ɗan wasan Chelsea mai shekara 23 Tammy Abraham, Aston Villa dai ta jima tana nuna zawarci a kansa, yayin da Wolves da Borussia Dortmund suka nuna kwadayinsu a kansa. (Football Insider)
Burnley na duba yiwuwar cimma yarjejeniyar £13m da ɗan wasan Lyon asalin Ivory Coast, Maxwel Cornet, wanda yanzu haka Hertha Berlinke nema.(Sun on Sunday)
Tottenham tana iya jefa Real Madrid cikin tsaka mai wuya kan ɗan wasan Faransa Jules Kounde da ke taka leda a Sevilla.(Sport)
Chelsea ta nuna sha'awar dauko Kounde kuma tana iya fin karfin Spurs wajen daidaitawa a wannan kakar. (Eldesmarque, via Sun on Sunday)
Tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane, mai shekara 49, zai yi watsi da bukatar rike wata kungiyar a yanzu.(L'Equipe - via ESPN)
Yarjejeniyar komawar Olivier Giroud daga Chelsea zuwa AC Milan ta tabbatar, bayan cimma yarjejeniyar shekara biyu da ɗan wasan mai shekara 34 ya yi da kungiyar ta Italiya. (Le Parisien - in French)
KocinEverton Rafael Benitez na son ya sayo ɗan wasan Barcelona Clement Lenglet. (Fichajes - in Spanish)
Karim Benzema mai shekara 33 zai ci gaba da zama a Real Madrid ko da kuwa kungiyar ta yi nasarar dauko Kylian Mbappe daga Paris St-Germain a wannan kakar. (Marca)
Watford ta zaku ta saye ɗan wasan Denmark Jens Stryger daga Udinese.(90mins)
Zakarar Italiya Inter Milan tayi nasara a fafatarwar saye dan wasan Shamrock Rover Kevin Zefi mai shekara 16, da kungiyoyi suka rinka zawarci ido rufe kama daga na Frimiya har zuwa Jamus da Netherlands. (Sun on Sunday)
Barcelona ta amince da yarjejeniyar sayen Carles Alena daga Getafe yayin da kungiyar ke kokarin rage kudaden da take kashewa don tilastawa ɗan wasan Argentina Lionel Messi, shiga wani sabon kwangilar. (Goal)
Ƙokarin Arsenalna sayen mai tsaron ragar Ajax Andre Onana, ya kamu da cikas bayan ɗan wasan Kamarun ya nuna cewa ya fi son zama a kungiyar Faransa, Lyon. (Football London)
Sampdoria na duba yiwuwar mika tayi kan dan wasan Scotland Ryan Christie daga Celtic. (Record)
Tottenham na da kwarin gwiwa a tayin da ta gabatar kan dan wasan Kamaru Carter-Vickers, duk da ninka kudin sayensa zuwa £5m. Kulob ɗin Newcastle United da Celtic duk sun nuna suna son saye shi. (Football Insider)












