Italiya ta lashe kofin nahiyar Turai na biyu a tarihi

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar kwallon kafa ta Ingila za ta ci gaba da neman lashe kofi a babbar gasar tamaula, bayan shekara 55, wadda ta kasa daukar Euro 2020 a bana.
Italiya ce ta doke mai masaukin baki Ingila a bugun fenariti da ci 3-2 a wasan karshe da suka kara a Wembley a gaban dubban 'yan kallo.
Duk da kwallo biyu da mai tsaron raga ya tare a bugun fenariti, Ingila ta barar da uku ta hannun Marcus Rashford da Jadon Sancho da kuma Bukayo Saka.
Wasan karshe a babbar gasar tamauala da Ingila ta buga tun 1966, sannan a gida a gaban 'yan kallo 60,000 an dakushe fatan da ta yi na cin kofi tun bayan shekara 55.
Ingila ce ta fara cin kwallo ta hannun Luke Shaw haka suka je hutu ba ci, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Italiya ta farke ta Leonardo Bonucci.
Haka wasan ya tashi 1-1 sai aka yi karin lokaci nan ma karawar ba a fidda gwani ba, dalilin da aka je bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Wadanda suka ci wa Italiya fenariti sun hada da Domenico Berardi da Leonardo Bonucci da kuma Federico Bernardeschi.
Wadanda suka kasa ci wa Italiya bugun daga kai sai mai tsaron ragar kuwa sun hada da Andrea Belotti da kuma Jorginho.
Ita kuwa Ingila ta ci nata bugun daga kai sai mai tsaron raga ta hannun Harry Kane da kuma Harry Maguire, yayin da Marcus Rashford da Jadon Sancho da kuma Bukayo Saka suka barar.
An fara gasar kofin nahiyar Turai a 1960 da Faransa ta fara karbar bakunci, wanda Soviet Union ta fara lashe kofin a lokaci.
Shekara takwas tsakani Italiya ta karbi bakunci ta kuma lashe kofin a karon farko, bayan da ta yi nasara a kan Yugoslavia.
Ingila wadda ta lashe kofin duniya a 1966, ba ta cib kofin nahiyar Turai ba, kuma tun kofin duniya ba ta sake lashe babban kofi a duniya ba, shekara 55 kenan.












