Manchester United: Magoya baya na son a kori Ole Gunnar Solskjær

Kocinn Manchester United

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Da yawa daga cikin magoya bayan kungiyar na kallon an bai wa kocin duk wata dama da ya kamata, amma har yanzu bai ci ko da kofin shan ruwa ba.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Magoya bayan Manchester United a fadin duniya na kiraye-kirayen a kori kocin kungiyar Ole Gunnar Solskjær.

Wannan ya biyo bayan rashin nasarar da kocin ya yi a wasa na shida na gasar Premier ta bana a gida a hannun Aston Villa.

Matasa da yawa sun rika wallafa abin da ke zukatansu na bacin rai a kafafen sada zumunta musamman Twitter.

Wannan kiraye-kirayen da magoya bayan suke yi, suna yin su ne karkashin maudu'i biyu, na farko shin ne #OleOut da kuma #SackOle.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Wani shafin magoya bayan United da ake kira da Planet Red@newtonheathyrc ya wallafa cewa ta wata fuskar kara tabarbarar da mu ya yi bayan kawo Sancho da Varane da kuma Ronaldo. A ce abu ba zai yiwu ba, ba wani abu ba ne eh!! #OleOut".

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Wani da ake kira Bagus rian@1mprovise shi ma ya wallafa cewa "Ole kana da kyau amma lokacin da za ka bar kungiyar ya yi,".

BBC
Bayanan hoto, Zidane da Conte su ake ganin za su iya maye gurbin Solskjær idan ya bar kungiyar

Bli putu@DanyNatakusuma shi ma ya wallafa bayani cikin wani hoto da ke cewa "magoya bayan United a halin yanzu".

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Baya ga neman a kori kocin da magoya bayan ke yi, a hannu guda kuma magoya bayan suna haska wa kungiyar akwai koci guda biyu a kasa Zidane da Antonio Conte.

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Mr_One ya ce "#OleOut a samo sabon koci #Zidane".

Kauce wa X, 5
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 5

Wannan da ake kira Ahmad Bilal @ahmadbmba85 cewa ya yi "ManUtd idan muna son mu ci kofina na yi imanin akwai bukatar kawo #Zidane. #Ole ba zai iya ci mana wasanni ba, muna rashin nasara a hannun kananan kungiyoyi, ka yi tunanin mai zai faru idan za mu yi wasa da Manchester City ko Chelsea ko kuma Liverpool. A gasar Zakarun Turai ya za ka buga da Real Madrid".

Caρтaιη Mкυυ🎖 @CaptainGerry_ ya ce "Barka dai ManUtd ku sanar da daukar wannan mutumin. Ku ba shi duk wata dama da yake bukata. #OleOut.

Kauce wa X, 6
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 6

Solskjær ya samu duk wata dama

Da yawa magoya bayan United suna ganin an bai wa Solskjær duk wata dama da ya kamata an ba shi a kungiyar.

Solskjær ya buga wasa 121 a United ya kuma ci 58 yayin da ya yi rashin nasara a 32 ya kuma yi canjaras a wasa 31 amma babu ko kofi guda da ya ci a kungiyar.

A halin da ake ciki yanzu ya yi rashin nasara a wasan farko na gasar Carabao inda West Ham ta yi waje da shi a gasar.

An cinye Manchester a wasan karshe na gasar Europa har sau biyu, rashin nasarar farko a Sevilla sannan kuma na biyu a hannun Villarreal.

A gasar Champions wasan United da RB Leipzig a 2020, wanda ake ganin bai kamata a cire kungiyar ba, bayan samun nasara a wasanni biyu na rukuni da ta yi.

Kafin wannan PSG ta cinye kungiyar wanda a 2019 wanda ake ganin laifin kocin ne saboda an bai wa dan wasansa na tsakiya Fred katin gargadi kuma yana ta yin duka amma yaki cire shi har aka ba shi jan kati.

A bara ya kare a matsayi na biyu a Premier wanda tun kan a kammala ya ce ya karaya da gasar.

Yan wasan da aka tara wa Solskjær ana ganin zai iya abin arziki da su a kowace irin gasa.

Kocin yana da Ronaldo da Cavani da Varane da Pogba da Bruno da dai sauransu wadanda aka amince cewa dukkansu masu kyaune.

Yanzu dai kalubalen da yake gaban kocin na wasannin da zai buga a nan gaba ana tsammanin ba zai iya tsallakewa ba da wannan jan cikin da yake.

Shafin B/R football ya wallafa wadannan wasanni da ake kallo a matsayin kalubalen da kungiyar za ta fuskanta a watan Oktoba da Nuwamba.

B/R

Asalin hoton, B/R

Tambayar da magoya bayan kungiyar suke yi shi ne, shin wannan kocin zai iya tsallake wannan siradin da yake gabansa?