Hazard da Bale na cikin 'yan Real da za su kara da Atletico

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta karbi bakuncin Atletico Madrid a wasan mako na 17 a gasar La Liga ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.
Wasan na hamayya na birnin Madrid, za a yi shi ne a lokacin da Real ke jan ragama da maki 39 wato tazarar maki 10 tsakaninta da Atletico, ta hudu a teburi.
Tuni kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan da za su karbi bakuncin Atletico a wasan na hamayya ciki har da Eden Hazard da Gareth Bale.
Haka kuma Karim Benzema wanda bai buga wasan da Real ta doke Sociedad 2-0 a karawar mako na 16 ba sakamakon jinya, yana cikin wadanda za su fuskanci kungiyar da Diego Simeone ke jan ragama.
Bale da Hazard manyan 'yan wasa ne a Real Madrid da suke karbar albashi mai tsoka, wadanda ke fama da jinya a kodayaushe.
Hazard ya buga minti 424 a kakar bana, sai dai minti tara kacal ya yi a wasa uku a baya. Rashin lafiyar da dan wasan ya kamu da ita lokacin da ya je buga wa tawagar Belgium wasa ta sa bai yi wa Real Madrid wasanni da yawa ba.
Haka kuma kwallo daya ya bayar aka zura a raga a kakar nan a wasan farko na buɗe gasar La Liga na karawa da Alaves, fafatawar da Real ta yi tare da Bale da kuma Benzema.
Shi kuwa Bale ya ci kwallo daya a wasan da Real ta doke Levante, daga baya ya ji rauni a mako na biyu cikin watan Satumba a wasansu da Celta Vigo kuma tun daga nan ba a sake jin sa ba.
Bale ya murmure daga baya, sai kuma ya kara jin rauni ranar 13 ga watan Nuwamba a lokacin da yake buga wa tawagar Wales wasa.
Watakila Real Madrid ta fuskanci wasan na hamayya da Benzema da Bale da kuma Hazard.
'Yan wasan Real Madrid
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Fuidias.
Masu tsaron baya: Carvajal, Militao, Alaba, Vallejo, Nacho, Marcelo, Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modric, Casemiro, Valverde, Lucas V., Isco, Camavinga.
Masu cin kwallye: Hazard, Benzema, Asensio, Jovic, Bale, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.












