Chelsea 1-4 Brentford: An yaga barakar Chelsea wadda za ta fuskanci Real Madrid

Antonio Rudiger

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Chelsea ta sha kashi a gida da ci 4-1 a hannun Brentford a wasan mako na 30 a gasar Premier League da suka fafata ranar Asabar.

Chelsea ta fara cin kwallo ta hannun Antonio Rudiger, bayan da suka koma daga hutu a wasan na hamayya da suka kece raini a Stamford Bridge.

Minti biyu tsakani Brentford ta farke ta hannun Vitaly Janelt, sannan Christian Eriksen ya zura na biyu a raga.

Daga baya Vitaly Janelt ya kara na uku kuma na biyu a ragar Chelsea, saura minti uku a tashi daga karawar ta 'yan birnin Landan Yoane Wissa ya ci na hudu.

Karon farko kenan da aka ci Chelsea kwallo uku ko fiye da haka a wasan hamayya a Stamford Bridge, bayan 3-0 da Arsenal ta yi mata a Afirilun 1997.

Wannan shine karon farko da Brentford ta yi nasara a Stamford Bridge tun bayan 1939.

Ranar 25 ga watan Fabrairun 1939, Brentford ta je gidan Chelsea ta yi nasara da ci 3-1 a gasar League ta 'yan rukunin farko.

Da wannan sakamakon Chelsea mai kwantan wasa tana ta uku a kan teburi da maki 59.

Brentford kuwa mai maki 33 tana ta 14 a kasan teburin Premier League na kakar nan.

Ranar 6 ga watan Afirilu, Real Madrid za ta ziyarci Chelsea, domin buga wasan farko a Champions League karawar quarterfinals.